Sunday, August 7, 2016

DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO

DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO - welcome to the blog Gadget Warrior, on this occasion we will discuss the information titled DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO as you are looking for, we have collect a lot of data to make this article so that you are satisfied with the information we convey, well please continue reading:

This is about : DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO
And this article : DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO
Article Hausa,

You can also see our article on:
BISMILLAHI..
 
A wannan karon ne akayi labarin tunawa da Sardaunar Saokoto Sir Ahmadu Bello da Kuma TAfawa Balewa Firemiyar Nigeria na farko. Shekaru Hamsin kenan da kashesu Allah ya jikansu. 

Idan na Kalli Nigeriya tambayoyi da yawa suna zuwa zuciyata, Mutanen Nigeriya suna son tunawa da mutanen kirki irin su sardaunar amman kuma mun gaza wajen koyi da halayensu. Mafi yawan lokaci ina tambayar kaina da ace wanda ya rasu zai iya dawowa me zai faru idan Sardauna ya dawo; me zai faru idan Tafawa Balewa ya dawo? Me zai faru idan Namandi Azikwe ya dawo; me zai faru idan Awolowo ya dawo?  Me zai faru idan mutane irin su Murtala Muhammad zasu dawo da sauran dai Mutanen kirkin Nigeria da akayi gwagwarmaya dasu.
Babu abin da zasu zo su tarar sai dai suzo suga mutanen da suka bari basu da hadin kai, zasu zo su tarar Arewacin Nigeria zaman lafiya yayi mata karanci. Zasu zo su rashin cin hanci da rashawa shine kan gaba a kasar amman kuma mafi yawan jaridun kasar basa buga labarin. Me yasa? Saboda basu suke juya akalar Jaridun ba.
A yanzu da nake muku Magana kasashen Afrika da dama basa zaman lafiya. Me zai faru idan wadannan mutanen kirkin suka dawo? Zasu zo su tarar muna yaki da junanmu, zasu zo su tarar mutane Nigeria suna siyo abin da suke da arzikinsu a cikin kasar kuma suna siyar da abin da basu dashi (Misali fetur). Zasu zo su tara da Yan Nigeriyan da basu son Kasarsu kuma basa son junansu. Zasu zo su tarar da Yan Nigeriyar da su su sardaunar suka sha gwagwarmaya don kada su zama bayin turawa, wannan karon da kansu yan Nigeriyan suke zuwa kasashen turawar don suyi bauta.

Zasu zo su tarar da yan Nigeria wanda basa alfahari da al’adarsu, kabilarsu ko kuma abubuwan da suka kera. Zasu zo su tarar da Yan Nijeriyan da zasu bude kamfani a cikin kasar amman sais u dinga sanya ma abin da suke kerawa Made in China (Wato anyishi daga China). Hatta Abinci yana da sunan turawa. Idan muka noma dankali sai muce masa Dankalin Turawa koda kuwa a Kudan ta jihar kaduna aka nomashi. Idan mun hada biredi da kosai sai muce masa sandswitch. Wannan sune yan Nigerian da zasu zo su tarar.
Za kuma suzo su tarar da Yan Nijeriyan da baza fadin labarin kansu kuma basa damuwa da jin labarin kansu; hatta gidajen jaridu sai dai su kalli CNN, Radio France, BBC, Aljazeera da sauransu bayan muna dasu NTA, Radiyoyin Jiha, Jaridun trust da sauransu. Zasu zo su tarar da yan Nijeriyan da basa jin dadin kansu. Idan suna son yin Nishadi sai dai dai su Kalli Manchester United, Real Madrid, Arsenal, Barcelona bayan muna dasu Kano Pillars, Rangers, Eyimba da sauransu.
Za kuma suzo su tarar da yan Nijeriyan da basu damuwa da wakokin gargajiya sai dai su mayar da hankalinsu wajen su 2pack, Shakira, Lil wayne da sauransu.
Me yasa bama tunama kanmu da wadannan abubuwan na Zahiri ne? Hatta rashin Lafiya dan Adam yake yi sai ya tafi America, Germany, USA bayan muna da manya manyan asibitoci. Indai baza mu canza ba babu inda zamu. Indai mun kasa tunani har abada baza mu canza ba.
Muna da manyan Jami’oi amman yaran masu kudi sai dai akaisu wata kasar. Muna da injiniyoyi amman manyan hanyoyinmu da gadojinmu duk yan China ne ke yinsu. Hakan yana nufin injiniyoyinmu ko hanya baza su iya yiba kenan? Muna da likitoci amman wasu daga yan siyasa da masu kudi da sunji suna rashin lafiya to ya danganta ne da kasar da mutum yake zuwa hutu. Idan kana zuwa hutu ingila ne sai kaje London, idan kana zuwa Spain ne sai kaje Madrid don kawai a duba lafiyarka. Hakan yana nufin bamu da imani akan akan likitocinmu kenan.
Manyan shugabanninmu sun kirkiro da hanyar ilimi kyauta amman suna daukar yaransu suna karatu a kasar waje. Hakan yana nufin su kansu basu yarda da makarantarmu ba kuma sun kasa gyarawa.
To Allah dai ya kyauta. Gashi muna son mu dinga tunawa da yan mazan jinya amman mu kanmu bamu yarda da kawunanmu ba. Mu kanmu bamu shaidar junanmu haka abin yake akan shagabanninmu.

ALHAMDULILLAHI....

 07035311650
SHARE AND COMMENT...


Articles DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO finished we discussed

A few of our information about the DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO, I hope that we submit article easy to understand

You've finished reading an article DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO and many articles about gadget in our blog this, please read it. and url link of this article is http://mallcopwarrior.blogspot.com/2016/08/da-ace-su-sardauna-da-ire-irensu-zasu.html Hopefully discussion articles on could provide more knowledge about gadgets.

Tag : ,
Share on Facebook
Share on Twitter
Share on Google+
Tags :

Related : DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO

0 comments:

Post a Comment